Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta yi watsi da rokon da takwararta ta Ingila ta yi na neman a tabbatar da komawar Adrien Silva zuwa Leicester City daga Sporting Lisbon.
Leicester ta mika takardun yarjejeniyar sayen dan Silva kan kudi fam miliyan 22 ne bayan dakika 14 da rufe kasuwar musayar 'yan wasa ranar 31 ga watan Augusta.
Fifa ta ki ta bayar da takardar shaidar cinikin Silva ta kasa da kasa, saboda haka 'yan Foxes ba su iya yi mi shi rijista ba.
Yanzu haka sai an bude kasuwar musayar 'yan wasa a watan Janairu ne Leicester za ta iya saka Silva a jerin 'yan wasanta.
Silva ya koma filijn wasan Estadio Jose Alvalade na Sporting ranar Lahadi kuma ya yi wa magoya bayan tsohuwar kungiyarsa ban kwana mai sosa rai kafin su buga wasan da suka tashi 0-0 da FC Porto.
Dan wasan ya kalli wasan Leicester City a filin wasan King Power, kuma ya yi aiki da masu horarwa na kungiyar a wurin motsa jiki na Belvoir Drive, amman an hana shi yin atisaye tare da 'yan wasan Leicester.
Source: BBC Hausa
Title :
Dole Leicester City Tajira Fifa Kan Maganan Adrien Silva
Description : Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta yi watsi da rokon da takwararta ta Ingila ta yi na neman a tabbatar da komawar Adrien Silva zuwa Leic...
Rating :
5