Wani alkali a Amurka ya dakatar da dokar shugaba Trump ta baya baya nan wadda ta hana baki daga wasu kasashe zuwa Amurka, jim kadan kafin ta soma aiki.
Dokar wadda aka sanar a watan jiya ta shafi matafiya daga kasashen Iran da Libya da Syria da kuma Yemen.
Sauran sun hada da Somaliya da Chadi da Koriya ta Arewa da kuma wasu mutane daga Venezuela.
Alkalin da ya yanke wannan hukunci a Hawaii ya ce dokar ta sabawa dokokin shige da fice na Amurka kuma bata gabatar da wata kwakwarar hujja a kan cewa mutanen da suka fito daga wadannan kasashe na musulmi shidda zasu yi barazana ga Amurka.
Fadar White House ta ce hukuncin na cike da kura kurai kuma ma'aikatar sharia ta ce za ta daukaka kara.
Source: BBC Hausa
Title :
Dokar Trump Kan Musulmi Tagamu Da Cikas
Description : Wani alkali a Amurka ya dakatar da dokar shugaba Trump ta baya baya nan wadda ta hana baki daga wasu kasashe zuwa Amurka, jim kadan kafin ta...
Rating :
5