Wani jigo a jam'iyyar APC mai mulki ta Najeriya, Injiniya Buba Galadima ya bayyana damuwa kan yadda jam'iyyar ta gaza gudanar da taron kwamitinta na amintattu kimanin shekara uku bayan kafuwarta.
"APC ba ta cancanci zama jam'iyya ba, tsarin mulkinta ya tanadi cewa sai kwamitin amintattu da kwamitin gudanarwa na kasa da kwamitin wakilan tsara manufofin jam'iyyar na kasa sun yi taro duk bayan wata uku.
Shin tun da aka kafa jam'iyyar nan, an yi taron kwamitin amintattu?"
Bugu da kari a cewarsa tun da aka kafa APC, jam'iyyar ba ta taba waiwayar kusoshin da suka kafa ta don jin ra'ayinsu game da nasarori ko akasin haka da ta samu ya zuwa yanzu ba.
Ya ce yana cikin mutum tara da suka sanya hannu don kafa ta, bisa wasu hujjoji da wasu sharudda, wadanda ya zuwa yau babu ko daya daga cikinsu da ta iya cimmawa.
Buba Galadima ya ce ba zai yiwu 'yan Najeriya su ci gaba da jiran jam'iyyar tsawon lokacin da ba su san karewarsa ba kafin ta farga ta zo ta jibanci lamarinsu.
Duk da rashin gamsuwa kan yadda jam'iyyar ke tafiya a yanzu, Buba Galadima ya bayyana kyakkyawan fatan cewa APC ko babu Shugaba Muhammadu Buhari za ta ci gaba da kasancewa.
"Ba na so ka dangantaka wannan jam'iyya da mutum daya, don kuwa jam'iyya ce tamu ta dukkan al'ummar Najeriya."
Ya ce sha'anin siyasa wani batu ne na wannan ya zo, wannan ya tafi, kuma duk wainar da aka tona, ba shakka akwai masu ci.
Source: BBC Hausa
Title :
Dani INEC Ne Dasai Na Rushe Jam'iyar APC-Buba Galadima
Description : Wani jigo a jam'iyyar APC mai mulki ta Najeriya, Injiniya Buba Galadima ya bayyana damuwa kan yadda jam'iyyar ta gaza gudanar da tar...
Rating :
5