Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin sa ba za ta iya soke cinikin kamfanin wutar lantarkin da gwamnatin Jonathan ta sayar da hannun jarin gwamnati ba, duk kuwa da cewa tsarin bai yi nasara ba.
Da ya ke magana jiya Alhamis a Abuja, a wurin Taron Tattalin Arziki, shugaban ya ce, ‘‘sayar da hannun jari abu ne mai wuyar sha’ani, wanda gwamnati ba ta iya tashi lokaci daya ta ce ta soke cinikin, saboda gudun abin da ka iya biyowa baya.”
Buhari wanda Karamar Ministar Kasafin Kudi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed ta wakilta, ya ce gwamnatin sa na so ta sake duba sayar da wutar lantarkin ne domin a sake samun shigo da masu hannayen jari da kuma sanin harkar ta yadda za su shigo su inganta tsarin sosai.
Buhari ya ce dukkan kamfanonin da su ka sayi hukumar wutar lantarki, ba su iya cimma kudirin da ake so ba na dalilin da ya sa aka sayar musu da ita.
Source: Premium Hausa
Title :
Dalilin Dayasa Bamu Soke Kamfanin Saida Wutan Lantarki Ba-Buhari
Description : Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin sa ba za ta iya soke cinikin kamfanin wutar lantarkin da gwamnatin Jonathan ta sayar da h...
Rating :
5