Wani matashi dan makaranta ya bindige takwarorinsa dalibai guda biyu a makarantarsu da ke Goiânia, kasar Brazil, a cewar kafofin yada labarai na cikin gida.
Yaron wanda ake jin dan shekara 13 ko 14 ne ya far wa 'yan makarantar tasu ne wadda ta kudi ce da tsakar rana.
Akalla wasu dalibai guda hudu kuma sun ji raunuka, inda aka garzaya da su asibiti a jihar Goiás, da ke tsakiyar kasar Brazil.
An ruwaito wani jami'in 'yan sanda na cewa mai yiwuwa an nuna wa yaron fin karfi ne, don haka tuni suka fara gudanar da bincike don gano ko hakan ne ya harzuka kai wannan hari.
Rahotanni sun ce wanda ake zargin iyayensa ko dai 'yan sanda ko kuma sojoji ne, ya koma gida inda ya zaro makaminsu kafin ya far wa abokan nasa.
Yanzu dai yaron yana hannun 'yan sanda.
Wani dalibi a ajinsu wanda ake zargin ya fada wa kamfanin dillancin labarai na Globo cewa yaron ya yi "fama da matsalar fin karfi".
"Wasu na toshe hanci idan ya nufo su, saboda ba ya amfani da turare," dalibin ya ce. "A lokacin da aka fito gajeren hutu, sai kawai aka ga ya fito da bindiga daga jakarsa ya fara harbi.
"Harbi kawai ya rika yi kan mai uwa da wabi. Don haka kowa ya yi ta kansa."
Harbe-harben makaranta irin wannan, nadiran ne a Brazil. Duk da yake, kasar na fama da yawaitar manyan laifuka, inda ake samun kashe-kashen gilla har kusan dubu 60 a shekara.
Source: BBC Hausa
Title :
Dalibi Ya Bindige 'Yan Ajinsu Guda Biyu
Description : Wani matashi dan makaranta ya bindige takwarorinsa dalibai guda biyu a makarantarsu da ke Goiânia, kasar Brazil, a cewar kafofin yada labara...
Rating :
5