Fati Garba shahararriyar yan wasan fina-finan Hausa ce da bata dade da shiga harakar ba. Sai dai shigar ta ke da wuya ta ko nuna hazakarta da kwazo wajen nuna cewa ita ma zata iya kara wa da manyan jarumai a farfajiyar fina-finan Hausa.
” Na dade ina neman yadda zan yi in shiga farfajiyar Fina finan Kannywood amma inaa tunda har sai da na hakura ma domin duk ta inda na bi sai kaga ba haka ba. Abin ya gagara.”
Fati ta ce dama can tana dan yin wasannnin kwaikwayo a jihar Neja inda tun a wannan lokacin take ta kokarin samun daman shiga Kannywood.
” Cikin Ikon Allah kuwa wata rana wani da nasani ya ce zai sakani a wani fim da yake shiryawa kuma Jarumi Adam Zango ne zai fito a fim din. Nan da nan ko naji kamar ya yi mini Albishir da miliyoyin kudi. Dalili kuwa shine, Adama Zango na daga cikin wadanda nake son in ko da gansu ne mu gaisa a rayuwa ta sai gashi wai zan hadu da shine sannan kuma har kila in yi fim tare da shi.”
” Da yake fim din A Zariya a kayi sai ko gashi na hadu da Adamu Zango. Daga nan ya ce mu hadu a Kaduna inda ya ke shirya wani fin din sa. Aiko muna haduwa sai gashi ya saka ni a ciki kuma ma babban matsayi ya bani. Daga nan kuwa sai likkafata ta ci gaba.”
Fati ta kara da cewa ko yanzu kasuwa ta tashi Dankoli ya ci riba domin da tayi hakuri burinta ya cika. Yanzu tana hidimar Bautar Kasa ce wato NYSC a Kaduna sannan ta ce babu abin da ta sa a gaba yanzu illa shirin Aure.
” Da za ran Allah ya kawo mini miji Zanyi Aure. domin shine yanzu a gabana. Kafinnan kuwa zan ci gaba da yin fim dina har zuwa lokacin.”
Ta jinjina wa jarumai kamar su Ali Nuhu, Aisha Tsamiya, Abdul Shareef, da Umar Shareef, Adam Zango wanda ta ce shine sila na kai wa ga cimma burinta, da sauran ‘yan wasan finan-finan Hausa da take aiki da su.
Source: Premium Hausa
Title :
Daga Kannywood Sai Miji-Fati Garba
Description : Fati Garba shahararriyar yan wasan fina-finan Hausa ce da bata dade da shiga harakar ba. Sai dai shigar ta ke da wuya ta ko nuna hazakarta d...
Rating :
5