Hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF ta bai wa Morocco damar karbar bakuncin gasar cin kofin Afirka ta 'yan wasan da suke taka-leda a nahiyar wato CHAN.
A ranar Lahadi hukumar ta amince ta bai wa Morocco damar karbar bakuncin wasannin maimakon Equatorial Guinea wacce ita ma ta yi takara.
Moroccon ta maye gurbin Kenya wacce hukumar kwallon kafar Afirka ta ce kasar ta kasa shirye-shiryen karbar bakuncin wasannin kamar yadda ya kamata.
Ana gudanar da gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 'yan wasan da ke buga tamaula a nahiyar tsakanin watan Janairu zuwa Fabrairun 2018.
Source: BBC Hausa
Title :
CHAN:An Baiwa Wa Morocco Karban Bakonci
Description : Hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF ta bai wa Morocco damar karbar bakuncin gasar cin kofin Afirka ta 'yan wasan da suke taka-leda a nah...
Rating :
5