Burundi ta kasance kasar ta farko a nahiyar Afirka da ta fice daga Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC.
Tun a bara ne dai kasar ta sanar da Majalisar dinkin duniya cewa za ta fice daga kotun.
Ha kuma wannan lamari ya tabbata a yanzu.
A yanzu dai ana yi wa wannan batu kallon zakaran gwajin dafi ga yunkurin samar da adalci ko shari'a a tsakanin kasa da kasa.
Batun dai ya ba mutane da dama mamaki.
kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun sha nuna adawarsu ga yunkurin wasu kasashen Afirka na ficewa daga kotun.
Kasashen dai na cewa kotun ba ta yi musu adalci, domin kuwa ba ta tuhumar sauran shugabannin kasashen duniya.
Sai dai kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta ce matakin da Burundi ta dauka,wani yunkuri ne,na hana dama ga wadanda aka ci zarafinsu a rikicin siyasar da ya faru a 2015, inda aka kashe mutane da dama.
Source: BBC Hausa
Title :
Burundi Ta Fice Da Kotun ICC
Description : Burundi ta kasance kasar ta farko a nahiyar Afirka da ta fice daga Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC. Tun a bara ne dai kasar ta sanar da...
Rating :
5