Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi al'ummar kasar sabbin alkawari yayin da yake musu jawabi a ranar bikin cikar kasar shekara 57 da samun 'yancin kai.
Shugaban ya yi wa dubban matasan kasar marasa aikin yi alkawarin ba su aiki, inda ya ce zai samar wa matasa dubu 10,000 aikin yi.
Sai dai wannan ba sabon abu ba ne, don ko a lokacin da yake yakin neman zabe ya taba yin irin wannan alkawari - abin da wasu suke ganin har zuwa yanzu bai cika ba.
Har ila yau shugaban ya yi alkawari game da wata matsala da ta dade tana ciwa 'yan kasar tuwo a karya wato matsalar karancin hasken wutar lantarki.
Ya yi alkawarin kara adadin wutar lantarkin da kasar take samarwa daga Mega Watt dubu 7,001 zuwa 10,000.
Sai dai sabanin alkawarin samar da ayyukan yi, shugaban ya ce yana fatan wadatuwar wutar lantarkin ne nan da shekarar 2020.
Hakazalika ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a yankin Neja-Delta (mai arzikin man fetur) don samun dawwamanman zaman lafiya a yankin.
Sai batun yaki da cin hanci da rashawa, wanda shi ma an saba ji shugaban yana shan alwashin magance shi a baya.
Ga kadan daga cikin ra'ayoyin ma'abota shafinmu na Facebook game da batun:
"Me jiya ta yi bare yau? Mun gaji da gafara sa ba muga kaho ba. Tsoho (Buhari) ka kauce kawai ka ba wa matasa filin su kawo canji," in ji Hudu Muhammad Huduwala.
Sai dai Bashir Sahal Nguru addu'ar fatan cika alkawuran ya yi:
"Hakika sabon alkawarin da Shugaba Buhari ya yi wa matasa na samar musu da ayyuka kimanin dubu goma a kowacce jiha, hakan shi ya nuna cewa shugaban na sane da dimbin matsalolin rashin aikin yi da matasa suke a ciki, da fatan Allah Ya ba shi cika alkawuran da ya dauka," in ji shi." Ko shakka babu na yi imanin cewa Shugaba Buhari zai iya ciki wannan alkawari da ya daukarwa matasan kasarmu tun da mun gani a shirin N-Power," a cewar Mustapha Marabar Musawa.
Amma ra'ayin Abubakar Sarina ya bambanta inda ya ce:
"Wannan alkawarin 'yan siyasa ne kawai wanda ake dauka ba a cikawa. A baya dai idan kafadi magana ina gasgatawa, amma yanzu na fara dawowa daga rakiyarka Buhari," in ji shi.
Source: BBC Hausa
Title :
Buhari Yayi Wa 'Yan Nigeria Sabbin Alkawura
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi al'ummar kasar sabbin alkawari yayin da yake musu jawabi a ranar bikin cikar kasar shekara 57 d...
Rating :
5