Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar, ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari a kan umarnin da ya bayar na biyan jami'an tsaron da suka yi yakin Biafra wadanda aka yi wa afuwa, hakkokinsu na fansho.
Atiku Abubakar wanda ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter ya ce, abin da Shugaba Buharin ya yi na nuna hadin kan Najeriya.
A ranar Laraba ne Shugaba Buhari ya amince da biyan fanshon ga jami'an 'yan sandan da gwamnatin Najeriya ta yi wa afuwa tun a shekarar 2000 lokacin mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo.
Wadannan 'yan sanda sun yi aiki ne a 'haramtacciyar' kasar Biafra a lokacin yakin basasar Najeriya da aka shafe watanni 30 ana yi.
Sai dai tun bayan da aka yi musu afuwar ba a biya su komai daga cikin kudaden fanshonsu ba.
A wata sanarwa da wata hukuma wadda ke kula da biyan fanshon ta fitar ta ce, za a biya mutum 162 yayin da mutum 57 kuma iyalansu ne za su karba a madadinsu a biyan farko da za a yi.
Hukumar ta kuma ce za a fara biyan farkon ne ranar Juma'a 20 ga watan Oktobar nan a birnin Enugu da ke Kudancin Najeriya.
Sai dai watakila wannan yabo da Atiku Abubakar ya yi wa Shugaba Buhari ya zo wa wasu da mamaki, ganin cewa a baya-bayan ya caccaki gwamnatin Buharin kan al'amura da dama da suka hada da korafin da ya yi na watsi da shi da aka yi a tafiyar da harkokin gwamnatin.
Source: BBC Hausa
Title :
Buhari Yana Son Hadinkan Nigeria-Atiku
Description : Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar, ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari a kan umarnin da ya bayar na biyan jami...
Rating :
5