Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yaba wa majalisar dokokin kasar game da ayyukan kwamitocinta wadanda suke sanya ido kan yadda ake tafiyar da ayyukan gwamnati.
Shugaban ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a jawabinsa na ranar bikin cika shekara 57 da samun 'yancin kasar.
Najeriya ta samu 'yancin kai ne daga hannun Turawan Birtaniya a shekarar 1960.
Shugaban ya ce zai samar da ayyukan yi ga matasa marasa aiki kimanin 10,000 a kowace jiha da ke kasar.
Ya ce zai yi hakan ne ta hanyar wani sabon shiri da Babban Bankin Kasar (CBN) zai bullo da shi.
Sai dai shugaban bai fadi tsawon lokacin da yake fatan cika alkawarin samar da ayyukan ba.
Har ila yau, shugaban ya ce ba zai taba amincewa da kiraye-kirayen da wadansu 'yan kasar suke yi na ballewa ba.
"A lokacin da nake matashin soja, na ba da gudummuwata tun daga farko har karshen yakin (Basasar Najeriya) wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum kimanin miliyan biyu, ya kuma haddasa asara da barna mai yawa," in ji Shugaba Buhari.
Ya ci gaba da cewa wadanda suke kiraye-kirayen maimaita hakan (a yanzu), "ba a haife su ba lokacin yakin don haka ba su da masaniya game munanan abubuwan da yakin ya jawo wa al'umma."
Hakazalika ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda wadansu jagorori a yankin da ke son ballewa "ba sa jan kunne matasan da suke ci gaba da ke son a raba Najeriya."
Daga nan shugaban ya ce sulhu shi ne mafita kan duk wani al'amari.
Sai dai ya bukaci "duk wanda yake da wani korafi game da kasar da ya gabatar da shi ga majalisar dokoki ta kasar da kuma majalisun dokoki na jihohi."
Shugaban ya yi hannunka mai sanda ga masu neman ballewar, inda ya ce ba mutum ya kai kokensa ga wadansu kungiyoyi "marasa kan gado ba."
Shugaban ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a yankin Neja-Delta don samun dawwamanman zaman lafiya a yankin.
"Muna da niyyar magance sahihan matsalolin al'ummomin yankin," in ji shi.
Kan batun tsaro
Shugaban ya yaba da wa dakarun kasar kan galabar da suke samu a kan mayakan Boko Haram.
"Dole mu gode wa zakakuran sojojinmu kan yadda suka fatattaki 'yan Boko Haram, suka samu nasara a kansu, kuma aka rage yawan hare-haren da ake kaiwa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba."
Daga nan ya ci gaba da cewa "ba za mu yi kasa a gwiwa ba," inda ya ce an fara fadada aikin rundunar Lafiya Dole da take aiki a yankin arewa-maso- gabashin kasar.
Har ila yau ya gode wa makwabtan kasashe da sauran kasashen duniya game da taimakon da suke ba "kasar a fagen yaki da ta'addanci."
Hakazalika ya ce gwamnatinsa tana "aiki ba dare, ba rana" wajen ganin an 'yanto sauran 'yan matan Chibok da sauran mutanen da ke hannun 'yan Boko Haram.
"Gwamnati za ta taimakawa dakarun kasar nan ba kawai a yaki da ta'addanci ba, amma har da matsalolin satar mutane don neman kudin fansa da fashi da makami da kuma rikicin makiyaya da manona," a cewarsa.
Tattalin Arziki
Shugaban ya bayyana shirye-shiryen da gwamnatinsa take yi wajen ganin kasar ta rage dogaro kacokan kan man fetur.
Hakazalika ya bayyana irin taimakon da gwamnatinsa take bayarwa a fannin aiki gona.
Daga nan ya tabo batun matsalar wutar lantarki, inda ya ce kasar tana da burin samar da Mega Watt 10,000 nan da shekarar 2020 daga adadin 7,001 da ake samarwa yanzu.
Shugaban ya ce wata bakwai ke nan a jere da hauhawan farashin kayayyaki yake ci gaba da raguwa a kasar.
Ya kuma tabo batun yadda darajar kudin kasar wato Naira take farfadowa idan aka kwatantata da dalar Amurka.
Sai batun yadda kasar take fitowa daga matsin tattalin arziki.
Cin hanci
Shugaban ya ce a shirye yake ya ga bayan matsalar cin hanci da kabar rashawa, kamar dai yadda ya saba shan alwashin yin hakan a baya.
Daga nan ya zayyana shirye-shireyen gwamnatinsa wajen magance matsalar.
Har ila yau shugaban ya yaba wa majalisar dokoki ta kasar game da ayyukan kwamitocinsu na sanya ido.
Ya kuma bukace su da su yi dokokin magance cin hanci.
A karshe ya bukaci daukacin 'yan kasar da su "yaki cin hanci ta hanyar kin ba da shi, da kuma karbarsa."
Source: BBC Hausa