Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ba da umarnin a kori tsohon shugaban kwamitin yin garambawul ga shirin fanshon kasar, AbdulRasheed Maina.
A wani sakon da aka wallafa a shafin Shugaban kasar na Twitter, Shugaba Buhari ya ce a kori Abdulrasheed Maina daga aiki nan take, a kuma yi bincike game da yadda akayi ya koma aikin gwamnati.
Kazalika, shugaban kasar ya ce umurci shugabar ma'aikatan gwamantin tarayyar Oyo-Ita Winifred Ekanem, ta mika rahoton binciken ga ofishin shugaban ma'aikata na fadar shugaban kasa, Abba Kyari, kafin a tashi daga aiki ranar Litinin, 23 ga watan Oktoba 2017.
A baya bayan nan dai masu fafutuka a Najeriya sun ce ya zama wajibi Shugaban Muhammadu Buhari ya kama tsohon shugaban kwamitin yin garambawul ga tsarin fanshon kasar AbdulRasheed Maina, in har da gaske yake yaki da cin hanci da rashawa.
Shugaban kwamitin da ke bai wa Shugaba Buhari shawara kan yaki da cin hanci da rashawa, Farfesa Itse Sagay, yana sahun gaban cikin masu kira ga shugaban Najeriyar ya sa a kama tare da hukunta AbdulRasheed Maina.
Farfesa Sagay ya ce ya kamata a hukunta duk wanda yake da hannu a mayar da AbdulRasheed Maina bakin aiki domin su ma sun taimaka wajen aikata laifi.
Baya ga Farfesa Itsey Sagay, fitaccen lauyan nan, Femi Falana, shi ma ya fito ya ce dole a kama AbdulRasheed Maina domin ya amsa tuhume-tuhumen da hukumar EFCC take masa.
Ya kuma ce ya zama wajibi a hukunta dukkan masu hannu a mayar da Maina aiki domin suna neman su hana ruwa gudu ne a yakin da shugaban kasar ke yi da cin hanci da rashawa.
A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce: "Ana mayar da wanda ake tuhuma da satar biliyoyin nairori bakin aiki, kuma kuna tunanin Buhari yana yaki da cin hanci da rashawa."
Ita dai hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (EFCC) ta fara neman Abdulrasheed Maina ruwa-a-jallo ne a shekarar 2015 kan zargin yin sama da fadi da naira bliyan biyu cikin kudin yin garam bawul wa tsarin fanshon Najeriya.
Bugu da kari, sanarwar da hukumar EFCC ta bayar cewar tana neman Maina har yanzu tana nan a shafinta na Intanet.
Source: BBC Hausa
Title :
Buhari Ya Tauna Tsakuwa
Description : Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ba da umarnin a kori tsohon shugaban kwamitin yin garambawul ga shirin fanshon kasar, AbdulRasheed M...
Rating :
5