Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi afuwar shugabannin majalisar dokokin Najeriya bisa hana su shiga fadarsa da jami'an tsaro suka yi a ranar Alhamis da daddare.
Jami'an tsaron fadar sun hana shugabannin majalisar shiga ne bisa dalilin cewa ba a ba su izinin barin su ba, suka kuma bukaci sai sun sauko daga motar safa da ta kai su don a bincike su daya bayan daya.
Wannan dalili ne ya sa shugabannin majalisar suka yi zuciya suka koma ba tare da shiga fadar ba.
Daga bisani bayan tafiyar shugabannin majalisar ne sai Shugaba Buhari ya tura shugaban ma'aikata na fadar shugaban kasa Abba Kyari, da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin majalisar dattawa Ita Enang, domin su ba su hakuri su kuma shigar da su fadar.
Sai dai wasu daga cikin shugabannin majalisar sun yi zuciya suka ki komawa, sai shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ne kawai suka koma.
BBC ta yi kokarin tuntubar bangaren fadar shugaban kasar amma ba ta samu jin ta bakinsu ba kawo yanzu, sai dai wata kwakkwarar majiya daga majalisar dokokin ta tabbatar mana faruwar lamarin, ta kuma ce tuni Shugaba Buharin ya bai wa 'yan majalisar hakuri kan abun da ya farun.
Tun farko dai Shugaba Buharin ne ya rubuta wasikar gayyatar shugabannin majalisar zuwa fadarsa don tattaunawa ta musamman da cin abincin dare.
Shugabannin majalisar da suka kai su 20 sun hada da shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai da mataimakansu da shugabannin masu rinjaye da na marasa rinjaye na majalisun biyu.
Wasu rahotanni sun ce bayan komawar shugabannin majalisar Shugaba Buharin ya kara ba su hakuri, ya kuma tabbatar musu cewa za a ba su takardar izinin shiga fadar a ko wanne lokaci suka so ba tare da shamaki ba.
A yanzu dai Shugaba Buharin ya sanya ranar Talata a matsayin sabuwar ranar da dukkan shugabannin majalisar za su koma fadar tasa don ganawa ta musamman din.
Source: BBC Hausa
Title :
Buhari Ya Nemi Afuwar Yan Malisa Kan Hanasu Ganinshi
Description : Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi afuwar shugabannin majalisar dokokin Najeriya bisa hana su shiga fadarsa da jami'an tsaro suka yi a ran...
Rating :
5