Shugaba Muhammadu Buhari ya kori Sakataren Gwamnatin kasar Babachir Lawal, inda ya maye gurbinsa da Boss Mustapha.
Shugaban kasar ya kuma kori shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta NIA Ambasada Ayo Oke.
Wata sanarwa da mai ba shugaban shawara kan yada labarai Femi Adesina ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da shawarwarin da kwamitin da ya binciki manyan jami'an gwamnatin biyu.
'Yan kasar sun dade suna jiran matakin da shugaban kasar zai dauka kan zarge-zarge da ake yi wa jami'an gwamnatin da almundahana.
Tun da farko an dakatar da Babachir ne saboda zargin saba ka'idojin bada kwangila karkashin shirin gwamnati na raya yankin arewa maso gabas wanda Boko Haram ta daidaita.
An kuma zarge shi da sama ka'idojin aikin gwamnati.
Shi kuwa Ambassador Oke ya gamu da fushin shugaban ne bayan da hukumar EFCC ta gano makuden kudade a wani gida a Legas.
Rahotanni sun ce hukumar NIA ta ce kudaden, kimanin Naira biliyan 13, nata ne, abin da ya haifar da rudani a kasar.
Dukkan mutanen biyu dai sun musanta zarge-zargen.
Shugaba Buhari ya kuma amince da kafa wani kwamitin musamman mai mambobi uku don yin nazari akan ayyukan hukumar NIA.
Sanarwar ta kara da cewa kwamitin zai bada shawarwarin yadda za'a inganta ayyukan hukumar tattara bayanan sirrin ta NIA.
A baya dai Jam'iyyun adawa a Najeriya sun yi zargin cewa gwamnatin Shugaba Buhari tana nuna son kai wajen yaki da cin hanci da rashawa.
Haka kuma wasu masu rajin yaki da cin hanci da rashawa sun yi alla-wadai da 'jan kafar" da suka ce shugaban na yi wajen hukunta wadanda ake zargin.
Me 'yan Najeriya ke cewa:
Wannan batu ya dade yana jan hakalin yan kasar inda suke bayyana ra'ayoyin daban daban.
Sadis Auwal Mai Lima- '' Wannan korar da shugaba Muhammad Buhari ya yiwa sakataren gwamnatinsa ya yi daidai haka muke so duk wanda ya ci amanar kasa kowaye shi a hukunta shi.''
Nura I. Sodangi-''Ba korar ta shi ba, mu ji cewa an bada umarnin gurfanar da shi kan zargin cin hanci da rashawa shi ne kawai za mu san da gaske ake yi.''
Yusufu Amos Goucho - ''Ya yi daidai amma akwai wadanda su ka yi laifi fiye da shi a cikin gwannatin saura suma a dauki mataki akan su''.
Kawo yanzu ba'a san matakin da shugaban kasar zai dauka ba bayan korar jami'an gwamnatin daga mukamansu.
Jama'a da dama za su zuro ido don ganin ko gwamnati za mika su ha hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa ko kuma korar ce kawai hukuncinsu.
Source: BBC Hausa
Title :
Buhari Ya Kori Babachir
Description : Shugaba Muhammadu Buhari ya kori Sakataren Gwamnatin kasar Babachir Lawal, inda ya maye gurbinsa da Boss Mustapha. Shugaban kasar ya kuma k...
Rating :
5