Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajanta wa iyalan daliban nan da ruwa ya ci a jihar Kaduna.
Ya kuma jajanta wa daukacin al'ummar jihar da kuma shugabanin makarantar da daliban suka fito.
A ranar Juma'a ne rundunar 'yan sandan jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ta tabbatar da cewa kogin Kaduna ya ci 'yan makarantar sakandare biyar masu ziyarar karo ilimi.
Rundunar ta bayyana cewa daliban da suka fito daga makarantar Victory International School, sun hau kwale-kwale daga wata tashar zuko ruwa ta hukumar samar da ruwan sha mallakar jihar kusa da tashar jirgin kasa da ke a lokacin da lamarin ya faru da su.
Bayan daliban su goma sun kammala ziyarar karo ilimin a tashar hukumar samar da ruwan ne sai suka hau kwale-kwale domin haye kogin a ranar Laraba.
Sai dai kwale-kwalen da suka hau din ya dare biyu domin yawan mutanen da ke kai, lamarin da ya sa daliban suka nutse.
Masu aikin ceto sun samu damar ceto biyar daga cikin daliban. An kuma samu gawarwakin biyu daga cikinsu yayin da har yanzu ake neman sauran gawarwakin.
Source: BBC Hausa
Title :
Buhari Ya Jajanta Wa Mutanen Kaduna
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajanta wa iyalan daliban nan da ruwa ya ci a jihar Kaduna. Ya kuma jajanta wa daukacin al'ummar ...
Rating :
5