Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin wadansu yara uku mata kanana wadanda ake cewa masoyan shugaban ne a fadarsa da ke Abuja.
Nicole Benson 'yar shekara 12 wadda ta fito daga jihar Legas da Maya Jamal 'yar shekara uku wadda take zaune a Abuja da kuma Aisha Gebbi mai shekara 10 wadda ta fito daga jihar Bauchi sun isa fadar ne tare da rakiyar iyayensu.
Yaran sun kwashe kimanin minti 30 a fadar shugaban kasar.
Kafofin yada labaran kasar sun sha ruwaito labarin daya daga cikin yaran wato Nicole a lokacin zaben shekarar 2015, inda suka ce ta taba tallafa wa shugaban da kudin abincinta.
Ba kasafai dai ake ganin shugaban yana ganawa da kananan yara ba.
Source: BBC Hausa
Title :
Buhari Ya Gana Da Yara Masoyansa A Fadarsa
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin wadansu yara uku mata kanana wadanda ake cewa masoyan shugaban ne a fadarsa da ke Abuja...
Rating :
5