Manazarta a Najeriya sun nuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari yana nuna wariya wajen yaki da cin hanci da rashawa a kasar.
Har ila yau sun ce daga cikin abubuwan da suka fi damun mutane ya zuwa yanzu sun hada da gaza inganta tattalin arzikin kasar yadda ya kamata.
"Domin haka, shirin da suka fito da shi sai aka ga ba wani abu takamaimai da zai tabbatar da cewa tattalin arzikin kasar zai habaka."
Haka zalika, ana ta diban bashi, wanda kuma a cewa manazartan ka iya gagarar Najeriya biya, don kuwa a cewarsu kudin shigar kasar ba wani karuwa ya yi ba.
Taron ya ce: "Gwamnati kamar wata dabara suke yi, suna cewa idan aka duba girman tattalin arzikin, bashin da ake ciyowa ba zai iya fin karfin kasar ba.
Amma idan ka duba kudin da suke shigowa nan ne za ka ga ba shakka akwai matsala, don kuwa duk wata kasa wadda yawancin kudin shigarta, ana amfani da su wajen biyan bashi.
Shi kenan babu abin da za a yi wa mutane aiki?"
Wadannan na daga cikin batutuwan da masana gami da masu ruwa da tsaki suka bijiro da su a wani taron kimanta nasarorin gwamnatin Muhammadu Buhari da ta shafe kusan shekara uku a mulki.
Akasarin ra'ayin mahalarta taron wanda cibiyar wanzar da ci gaba da kuma dimokradiyya a Najeriya ta shirya, shi ne babu wani ci gaban a-zo-a-gani da 'yan kasar suka shaida tun bayan kafa gwamnati.
Da yake shaida wa BBC sakamakon da taron ya cimma, wani wakili a cibiyar, Farfesa Jibrin Ibrahim ya ce karuwar garkuwa da mutane a kasar ta dusashe nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu ta fuskar tsaro.
"A kan tsaro, an dan samu zaman lafiya, amma har yanzu ana kashe-kashe. Mutane a yankin arewa maso gabas har yanzu samun matsalar Boko Haram.
Batun garkuwa da mutane kuma a fadin kasar ya zama ruwan dare, har ta kai mutane ma na tsoron tafiye-tafiye."
'An fara samun mafita kan tattalin arziki'
A cewar taron, idan aka duba an samu gyara ta wani fanni, ta wani fannin kuma sai a ga abubuwa ma na kara lalacewa ne.
Game da batun cin hanci da rashawa kuma, Farfesa Jibrin Ibrahim mutane sun yi tambayar cewa me ya sa idan makusantan Buhari sun yi laifi sai ya yi shiru?
"Mutane da yawa sun yi magana a kan tsohon Sakataren Gwamnati, Babachir wanda fiye da wata shida kenan aka yi bincike kansu, kuma aka ba shi rahoto kuma ya yi tsit a kan abin."
Farfesa Jibrin ya ce tambayar da mutane ke yi ita ce me ya sa idan abokansa ne ko aminansa, suka yi laifi yake yin tsit, wato kenan su doka ba za ta shafe su ba ke nan?
Source: BBC Hausa
Title :
Buhari Na Nuna Wariya Wajen Yakan Cin Hanci-Farfesa Jibrin
Description : Manazarta a Najeriya sun nuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari yana nuna wariya wajen yaki da cin hanci da rashawa a kasar. Har ila yau sun ce...
Rating :
5