Asirin wani matashi da budurwarsa ya tonu bayan ganowa da akayi cewa ya hada baki da ita domin su damfari iyayen yarinyar ne.
Ita dai yarinyar mai suna Tohebat ta hada baki ne da saurayinta wanda mai gadin wani gida ne mai suna Afolabi da ya boyeta sannan ya sanar da iyayenta cewa ya sace ta ne su aiko da naira 200,000 don fansanta.
Bayana Afolabi ya kira iyayen yarinyar ne fa sai ko uban yarinyar ya sanar da ‘yan sanda. Daga nan ko suka fara binciken sirri a kai.
Ba da dadewa ba kuwa sai suka gano cewa saurayin ta ne ya boye ta.
Da aka kamo su duka sai aka gano cewa ita yarinyar ne ta hada baki da saurayinta domin aikata wannan mummunar aiki.
Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Ahmed Illiyasu ya yi kira ga iyaye da su yi wa ya’yansu tarbiyar nagari gudun kada su fada irin haka.
Source; Premium Hausa
Title :
Budurwa Tahada Bakida Saurayinta Yasace Iyayenta Don Subiya Kudin Fansa
Description : Asirin wani matashi da budurwarsa ya tonu bayan ganowa da akayi cewa ya hada baki da ita domin su damfari iyayen yarinyar ne. Ita dai yarin...
Rating :
5