Amurka ta fara cire yawancin takunkumin tattalin arziki da ta sanya wa Sudan shekara 20 da ta wuce, saboda abin da ta kira matakan kyautata batun kare hakkin dan adam da kuma kokari a yaki da ta'addanci.
Jami'an Amurkar sun ce Sudan ta samu ci gaba a fannin kiyaye 'yancin dan adam, tare kuma da bayar da hadin kai a yaki da masu tsananin kishin Islama.
Sudan ta kasance wadda ta yi fama da takunkumin hana ta kasuwanci da kuma sauran takunkumi na gudanar da wasu harkokin daga Amurka.
Gwamnatin Amurka ta fara kakaba wa Sudan takunkumi shekara 20 da ta wuce, bayan da ta ayyana gwamnatin kasar a matsayin mai daukar nauyin ta'addanci.
A shekarun 1990 Sudan ta bayar da mafaka ga Osama bin Laden da kuma Carlos the Jackal.
Amurkar ta kara sanya mata wasu karin takunkumin a shekara ta 2007 a sakamakon rikicin yankin Darfur, inda shugaban kasar Omar al Bashir yake fuskantar tuhuma kan laifin kisan kiyashi.
To amma a yanzu Amurka ta sassauto a kan Sudan din saboda hadin kan da take bayarwa a yaki da masu tsattsauran ra'ayin Islama.
Haka kuma akwai alamun kokarin da ake na magance rikicin cikin gida a Sudan din da kuma bayar da damar kai kayan agaji ga jama'a.
Sai dai kuma kungiyoyin kare hakkin and adam na nuna matukar bacin ransu a kan wadannan matakai na sassauta wa Sudan da Amurka ke dauka a yanzu.
Kungiyoyin na korafi da cewa cire takunkumin zai iya jawo karin cin zarafin dan adam daga kasar, kuma Sudan ba ta taba mayar da hankali wajen kawo wani sauyi na gaske ba.
Baya ga kuma cewa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya na neman shugaban kasar, al Bashir shekara bakwai da ta wuce.
Source: BBC Hausa
Title :
Amurka Tafara Cirewa Sudan Takunkumi
Description : Amurka ta fara cire yawancin takunkumin tattalin arziki da ta sanya wa Sudan shekara 20 da ta wuce, saboda abin da ta kira matakan kyautata ...
Rating :
5