Sarki Salman na Saudiyya ya fara ziyarar aiki a kasar Rasha a ranar Alhamis, wannan ne karon farko da wani sarki zai kai ziyara kasar.
Sarki Salman ya ce kasashen biyu wadanda su ne suka fi fitar da danyen mai za su ci gaba da yin aiki domin daidaita kasuwar man.
Sarkin ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da Shugaban Rasha Vladimir Putin a birnin Moscow
Har ila yau shugabannin sun tattauna a kan batun kasashen Syria da Iraqi da kuma Iran - wadda Sarkin ya sake zargi da yin shisshigi a yankin gabas ta tsakiya.
A ranar Laraba, Mista Putin ya ce za a iya tsawaita wata yarjejeniyar duniya ta rage yawan man da ake hakowa domin daga farashin mai har ya zuwa karshen shekara mai zuwa.
Source: BBC Hausa
Title :
Saudiyya Da Rasha Zasuyi Aiki Tare
Description : Sarki Salman na Saudiyya ya fara ziyarar aiki a kasar Rasha a ranar Alhamis, wannan ne karon farko da wani sarki zai kai ziyara kasar. Sark...
Rating :
5