Sakamakon farko na gwajin alluran rigakafin cutar Ebola har iri biyu, ya nuna cewa duka biyun na iya kare mutane daga daukar cutar tsawon akalla shekara guda.
An gudanar da binciken ne a kasar Liberia inda aka gwada rigakafin kan marasa lafiya dubu daya da dari biyar.
Wadanda aka yi wa rigakafin sun samu kariya daga daukar cutar tsawon shekara guda.
Gwajin ya nuna cewa ana iya amfani da rigakafin wurin ceto rayukan al'umma duk lokacin da annobar Ebola ta sake barkewa nan gaba.
Cutar Ebola dai ta kashe fiye da mutum dubu 11 a yammacin Afrika a shekarar 2014.
Source: BBC Hausa
Title :
Ansami Rigakafin Cutar Ebola
Description : Sakamakon farko na gwajin alluran rigakafin cutar Ebola har iri biyu, ya nuna cewa duka biyun na iya kare mutane daga daukar cutar tsawon ak...
Rating :
5