Fiye da mutum 20 ne suka rasa rayukansu yayin da wadansu kimanin 200 suka jikkata bayan wani hari da aka kai a wani gidan rawa a birnin Las Vegas na jihar Nevada da ke kasar Amurka.
Maharin ya fara bude wuta ne daga hawa na 32 na benen wani otel mai suna, Mandalay Bay Hotel, inda ya hari wani wuri da ake wasan raye-raye.
'Yan sanda sun ce an harbe maharin wanda dan unguwar ne, kamar yadda suka ce.
Sai dai sun ce suna ci gaba da farautar wani wanda suke zargin yana aiki tare da maharin.
Daruruwan mutane sun tsere daga wurin kuma an rika jin karar harbe-harbe a wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta.
Hakazalika an samu rahotannin faruwar wadansu hare-hare a wasu bangare na birnin, sai dai 'yan sanda sun ce sun yi amannar cewa maharin shi kadai ne.
Wadansu mahalarta taron yayin da suke kokarin buya
Wadansu jirage sun fasa sauka a birnin bayan samun labarin harin.
Tun ranar Juma'a ake ta shagulgulan raye-raye a otel-otel da ke birnin.
Source: BBC Hausa
Title :
Ankashe Mutum Hamsin Awani Gidan Rawa A Las-Vegas
Description : Fiye da mutum 20 ne suka rasa rayukansu yayin da wadansu kimanin 200 suka jikkata bayan wani hari da aka kai a wani gidan rawa a birnin Las ...
Rating :
5