Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa kungiyar Manchester City ce za ta lashe gasar Premier na kakar bana, yayin da Liverpool da kuma Arsenal za su kasa zuwa gasar Zakarun Turai.
Kamfanin Gracenote Sports ne ya fitar da hasashen.
Har ila yau hasashen ya ce kungiyar Crystal Palace za ta fadi a gasar Premier.
Sai dai an fitar da hasashen ne bayan an buga wasa bakwai a kadai a gasar a bana.
Kamfanin ya ce Manchester City tana damar lashe gasar ne da kashi 47 cikin 100, yayin da United take da 24 cikin 100, ita kuma Chelsea tana da kaso 13 cikin 100.
Chelsea dai ita ce lashe gasar a kakar bara, amma kawo yanzu Manchester City take saman teburin gasar.
Source: BBC Hausa
Title :
Bincike Ya Nuna Man City Ne Zata Lashe Premier Ingila
Description : Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa kungiyar Manchester City ce za ta lashe gasar Premier na kakar bana, yayin da Liverpool da kuma Ar...
Rating :
5