Gwamnatin jihar Sokoto ta kafa kwamiti don samar da da za abi don warware matsalolin da fanni ilimi a jihar ya ke fama dashi.
Shugaban kwamitin Shadi Sabeh ya ce kashi 31 bisa 100 na malaman dake koyar wa a makarantun gwamnatin jihar basu da cikaken ilimin koyar da dalibai.
Da yake mika rahoton kwamitin nasa, Shadi ya ce ya zama dole gwamnati ta horas da malamai 548 da suke koyar wa a kauyukan jihar domin su kara kwarewa. Bayan haka kuma ya bada shawara a koyar da malaman ilimin komfuta domin sama da kashi 70 na malaman basu da wannan ilimi.
Gwamna Aminu Tambuwal ya godewa kwamitin kan aikin da yayi.
Ya ce za su tsaro hanyoyin da malaman za su dunga samun horo yadda ya kamata.
” Ba za mu kori kowa daga kan aikin sa ba, zamu horar da duk malaman sannan wadanda ba za su horu ba a fannin koyar wa za mu kai su fannin da za su yi amfani’’.
Source: Premium Hausa
Title :
Bazamu Kori Malami A Jihar Sokoto Ba,Zamu Horas Dasu Ne-Tambuwal
Description : Gwamnatin jihar Sokoto ta kafa kwamiti don samar da da za abi don warware matsalolin da fanni ilimi a jihar ya ke fama dashi. Shugaban kwam...
Rating :
5