Babbar jami'a mai bai wa shugaban Najeriya shawara a kan harkokin 'yan kasar da ke zaune a kasashen waje, Honourable Abike Dabri, ta ce, an kashe 'yan Najeriya hudu a cikin makwanni uku a Africa ta Kudu a hare-haren nuna kyama da ake kai wa 'yan kasar a wasu kasashe.
Kalaman nata na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomi a India su ka kama mutum biyar da ake zargi da lakadawa wani dan Najeriya dukan kawo wuka bisa zargin sata bayan wani hoton bidiyo da yayi ta yawo a intanet.
Abike Dabiri, ta ce tun bayan da suka samu labarin abinda ya faru da dan Najeriyar a India, suka tuntubi ofishin jakadancin Najeriyar da ke India, inda ya ce ana bibiyar lamarin har ma hukumomin kasar ta India sun fara daukar mataki.
Ta ce a yanzu haka an kama mutanen da ake zargi da hannu a kan wannan lamarin.
Babbar jami'ar ta ce sun bukaci kasar India da ta hukunta wadanda aka tabbatar suna da hannu a wannan aika-aikar da aka yiwa dan Najeriya domin sun dauki doka a hannunsu ne abinda kuma bai da ce ba.
Abike Dabiri ta ce daga shekarar 2015 zuwa yanzu an kashe 'yan Najeriya 116 a Afirka ta Kudu, kuma fiye da rabinsu 'yan sanda ne suka kashe su.
Don haka ta ce, gwamnatin Najeriya ba zata amince da kisan da ake yiwa 'yan kasarta dake zaune a wasu kasashe ba, shi ya sa ta ke bukatar kasashen da ake cin zarafin 'yan Najeriya a can da su rinka daukar matakan da suka dace a kan wadanda ke aikata laifin, koda kuwa jami'an tsaro ne.
Abike Dabiri, ta ce rashin hukunta masu aikata irin wannan laifin, shi ke sa ake cigaba da aikata laifin, amma da ana hukunta su yadda yakamata da za a samu raguwar aikata laifin.
Source: BBC Hausa
Title :
Bazamu Amince Da Kisan 'Yan Nigeria A Wani Kasa Ba-Buhari
Description : Babbar jami'a mai bai wa shugaban Najeriya shawara a kan harkokin 'yan kasar da ke zaune a kasashen waje, Honourable Abike Dabri, ta...
Rating :
5