Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona na taka rawar gani a kakar wasan kwallon kafa ta bana ta 2017/18.
Barcelona ta ci wasa bakwai da ta yi a La Ligar da ake yi, ta kuma ci wasa biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champion League, jumulla ta ci karawa tara kenan.
Hakan ya sa kungiyar tana ta daya a kan teburin La Liga da maki 21, ita ce kuma ke kan gaba a rukuni na biyu a gasar Zakarun Turai ta Champions League.
A wasa taran da ta yi ta ci kwallo 27 an kuma ci ta guda biyu kacal.
Tun fara kakar bana a Turai, PSG ta ci karawa tara a wasa 10 da ta yi, ta kuma yi canjaras sau daya.
Source: BBC Hausa
Title :
Barcelona Nataka Rawar Gani A Kakar Bana
Description : Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona na taka rawar gani a kakar wasan kwallon kafa ta bana ta 2017/18. Barcelona ta ci wasa bakwai da ta yi a...
Rating :
5