Tsohuwar jarumar fina-finan Kannywood Mansura Isa ta ce ba ta kewar rashin fitowa a fina-finan saboda sai da ta kai kololuwar ganiyarta kafin ta daina yin fim.
"Ina ganin ba na kewar fitowa a fim. Na kai karshen ganiyata kafin na bar Kannywood. Na samu nasarori da dama; na gina gida na kaina, na sayi mota, na je Umra, hasalima na auri jarumin Kannywood.
"Me zan ce bayan haka idan ba godiya ga Allah ba", in ji Mansura a hirar da ta yi da jaridar Premium Times wacce ake wallafawa a intanet.
Tsohuwar jarumar, wacce ta ce ita ce edita ta farko a masana'antar Kannywood, ta kara da cewa ta daina fitowa a fina-finan ne lokacin da ta yi aure saboda ta kula da iyalinta.
A cewarta, yanzu ba ta kallon fina-finan na Kannywood saboda ba ta da isasshen lokaci na yin hakan.
"Ina kallon fim ne kawai idan yana da matukar inganci. Amma ina kallon fina-finan series da ake nunawa a gidajen talbijin", in ji Mansura.
Ta ce zai yi wuya ta koma fitowa a fina-finai saboda yanzu tana gudanar da wata gidauniya, "ko da yake ana biya na na rubuta fina-finai na bai wa mashu shirya fina-finai su yi fim a kansu".
Mansura ta ce jaruman yanzu sun fi na da irinta kokari saboda akwai tsaro mai kyau kan yadda ake yin fina-finai a yanzu.
"Mun sha wuya matuka lokacin da muke fitowa a fina-finai; babu tsari mai kyau, babu ci gaban fasaha, muna fitowa a fina-finai ne kawai domin debe kewa. Ina so na gaya maka cewa na sha fitowa a fina-finan da ba a rubuta ba.
Mai shirya fim ne kawai zai gaya min abin da zan fada da baki. Amma yanzu ana bai wa jarumai rubutaccen fim din da za su fito domin su yi bitar abin da za su fada wata da watanni kafin a soma nadar fina-finan", in ji tsohuwar jarumar.
A yanzu dai Mansura ta fi mayar da hankali ne wajen kula da iyalinta da kuma kula da wata kungiyar agaji mai zaman kanta da ta kafa mai suna Today's
Source: BBC Hausa
Title :
Bani Kewar Yin Fina Finan Kannywood-Mansura Isa
Description : Tsohuwar jarumar fina-finan Kannywood Mansura Isa ta ce ba ta kewar rashin fitowa a fina-finan saboda sai da ta kai kololuwar ganiyarta kafi...
Rating :
5