Wani mummunan harin bam ya kashe mutum 30 a wata unguwa mai cinkoson jama'a a babban birnin kasar Somaliya, Mogadishu, kamar yadda 'yan sanda suka bayyana.
Hakazalika wadansu mutane da dama sun jikkata lokacin da wata babbar motar kaya da aka daura wa bama-bamai suka fashe a kofar shiga wani otel.
'Yan sanda sun ce mutum biyu sun mutu a wani hari na biyu a wata unguwa mai suna, Madina wadda take birnin.
Sai dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin tukuna, amma birnin ya saba fuskantar hare-haren kungiyar al-Shabab wadda take yaki da gwamnatin kasar.
Bayan harin farko, jami'in dan sanda Mohamed Hussein ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa: "An yi amfani da wata babbar mota ne wajen kai harin. Ba mu san adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba tukuna saboda har yanzu wuta ce ke ci gaba da ci a wurin."
Wadanda suka shaida al'amarin sun shaida wa BBC cewa mutane da dama ne suka rasa rayukansu.
Wakilin BBC ya ce ginin Safari Hotel ya ruguje, kuma ana zaton ya danne mutane da dama.
Wani mazaunin unguwar Muhidin Ali ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa: "wannan ne harin bam mafi muni da na taba gani, harin ya lalata duka wurin".
Source: BBC Hausa
Title :
Bam Yakashe Mutane 30 A Somalia
Description : Wani mummunan harin bam ya kashe mutum 30 a wata unguwa mai cinkoson jama'a a babban birnin kasar Somaliya, Mogadishu, kamar yadda '...
Rating :
5