Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Borno ta tabbatar da mutuwar mutum 14 baya ga 'yan kunar-bakin-wake uku a harin da suka kai Muna Garage a wajen birnin Maiduguri.
'Yan kunar-bakin-waken wadanda hukumomi suka ce duka mata ne, sun kai harin ne da maraicen ranar Lahadi, inda guda ta tayar da bam din ta, kuma daya ta fadi amma dai bam din bai fashe ba.
Sai dayar kuma ta sulale ta shiga gari lamarin da ya sa jami'an tsaro suka shiga farautarta ko da yake babu tabbacin ko akwai bam a jikinta ko kuma ta cire.
Ya zuwa yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin kai wannan hari, amma dai kungiyar Boko Haram ta yi kaurin suna wajen far wa birnin Maduguri ta hanyar amfani da kananan yara.
Shugaban hukumar agajin gaggawa ta jihar SEMA, Injiniya Satomi Ahmed, ya ce harin ya kuma jikkata karin mutum 17, wadanda ya ce hukumarsa ta kwashe su zuwa asibiti.
Ya ce mutane sun koma bakin harkokinsu wayewar garin Litinin, yayin da matasa 'yan sintiri suka killace yankin, su kuma sojoji na gudanar da bincike don gano yadda aka yi har maharan suka kutsa kai yankin.
A cewarsa a shekarar nan kadai, an kai harin kunar-bakin-wake Garejin Muna sau 13, sai dai babu wanda aka fi samun mutuwa kamar na ranar Lahadi.
Harin dai ya zo ne bayan samun lafawar hare-haren 'yan ta-da-kayar-baya a yankin, sakamakon matsa kaimin da dakarun tsaron kasar suka yi wajen dakile Boko Haram.
A karshen watan Yuli ne, Mukaddashin Shugaban kasar Yemi Osinbajo ya umarci manyan hafsoshin tsaron Najeriya su koma birnin Maiduguri da zama.
Manyan hafsoshin tsaron sun tare a can din ne bayan wani mummunan hari da kungiyar Boko Haram ta kai wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 40.
Source: BBC Hausa
Title :
Bam Bai Sunkashe Mutane 14 A Maiduguri
Description : Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Borno ta tabbatar da mutuwar mutum 14 baya ga 'yan kunar-bakin-wake uku a harin da suka kai Muna G...
Rating :
5