Asusun lamuni na duniya, IMF, ya ce tattalin arzikin duniya ya fara murmurewa amma akwai yiwuwar sake durkushewarsa.
Rahoton ya biyo bayan nazarin da asusun ya yi, wanda ya nuna cewa an samu farfadowar tattalin arziki a fadin duniya mai tattare da kalubale.
IMF ya ce yanzu masu cin bashi za su iya biyan rance ba tare da shiga matsala ba, abinda zai sa masu bayar da bashi samun riba.
Sai dai kuma asusun ya ce karancin kudin ruwa da sauran manufofin bankuna da ke bai wa masu cin bashin damar biya za su iya sauyawa da zarar tattalin arzikin ya karasa murmurewa.
Idan aka samu wannan sauyi in ji IMF, kudin ruwa zai karu, masu cin bashi su kasa biya, don haka masu bada rance za su kwana a ciki, abinda zai iya haddasa sake tabarbarewar tattalin arzikin.
Source: BBC Hausa
Title :
Babu Tabbas A Farfadowar Tattalin Arzikin Duniya-IMF
Description : Asusun lamuni na duniya, IMF, ya ce tattalin arzikin duniya ya fara murmurewa amma akwai yiwuwar sake durkushewarsa. Rahoton ya biyo bayan ...
Rating :
5