A daidai lokacin da ake dakon sake babban zaben Kenya, wata babbar jami'ar hukumar zaben Kenya, Roselyn Akombe, ta yi murabus tana mai cewa kasar ba za ta iya gudanar da sahihin zabe ba a mako mai zuwa.
Roselyn ta ce hukumar zaben kasar (IEBC) tana cikin wani matsi na siyasa, kuma ba za ta iya yanke shawara ba.
Jami'ar, wadda a yanzu haka tana Amurka ne, ta shaida wa BBC cewa ta ji tsoron wani abu na iya faruwa da ita a lokacin da take Kenya saboda an yi mata barazana sosai.
A makon da ya gabata ne, shugaban 'yan adawa, Raila Odinga, ya janye daga zaben shugaban kasar da za a sake yi ranar 26 ga watan Oktoba.
A wata sanarwa da ta fitar, Mis Akombe ta ce ta shiga cikin tsananin damuwa kan daukar matakin barin hukumar zabe ta IEBC.
"Matakin da na dauka na yin murabus zai bata wa wasun ku rai, amma ban yi hakan saboda gazawa ba.
"Na yi bakin kokarina. Wasu lokutan dole ka hakura da wasu abubuwan musamman idan akwai barazana ga rayuwa. Hukumar ta zama wani bangare na rikicin da ke faruwa yanzu haka. Hukumar na cikin rudani.
"A yadda hukumar nan take a yanzu ba za ta iya tabbatar da aiwatar da sahihin zabe ba ranar 26 ga watan Okotoba."
Babu tabbas kan tasirin da wannan mataki nata zai yi kan makomar zaben.
Source: BBC Hausa
Title :
Babban Jami'ar Hukumar Zaben Kenya Tagudu Amurka
Description : A daidai lokacin da ake dakon sake babban zaben Kenya, wata babbar jami'ar hukumar zaben Kenya, Roselyn Akombe, ta yi murabus tana mai c...
Rating :
5