Wasu masu fafutika a Najeriya sun soki kamun ludayin Shugaban Kasar Muhammadu Buhari kan yadda yake tunkarar yaki da cin hanci da rashawa a kasar, suna cewa idan ana batun yaki da cin hanci da rashawa, babu bambanci tsakanin gwamnatinsa da ta tsohon Shugaba Goodluck Jonathan.
Masu sukar lamarin shugaban kasar dai na kafa hujja da wasu bincike da aka gudanar na zargin wasu jami'an gwamnati da aikata almundahana, amma shugaban kasar ya kauda da kansa.
Har ila yau sun ba da misali da rashin daukar matakai bayan ya karbi rahoton binciken sakataren gwamnatin tarayya da aka dakatar Mista Babachir David Lawal.
Da da kuma batun daraktan hukumar leken asiri ta kasar NIA, Ayo Oke tare da wasu jami'an gwamnatin kasar da ake zargi da cin hanci da rashawa.
Auwal Musa Rafsanjani, wakili a kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya ta Transperancy International ya shaida wa BBC damuwarsu:
Latsa alamar lasifika da ke hoton samadon sauraron cikakkiyar hirar da Rafsanjani ya yi da BBC
Source: BBC Hausa
Title :
Ba Bambanci Tsakanin Gwamnatin Buhari Dana Jonathan-Rafsanjani
Description : Wasu masu fafutika a Najeriya sun soki kamun ludayin Shugaban Kasar Muhammadu Buhari kan yadda yake tunkarar yaki da cin hanci da rashawa a ...
Rating :
5