Aure da yin abokai ko kawaye na kukut ka iya taimakawa wajen hana kamuwa da cutar mantuwa a cewar masu bincike na Jami'ar Loughborough a Ingila.
Binciken wanda aka wallafa a Mujallar kimiyyar nazarin tsufa, ya bibiyi rayuwar manyan mutane guda 6,677 tsawon kimanin shekara bakwai.
Dankon zumuncin da ke tsakaninn rukunin abokan mutum na kukut ga alama ya fi muhimmanci a kan yawan abokai, a cewar ayarin masu bincike.
Gidauniyar Alzheimer's Society mai tallafa wa masu cutar shiriricewa ta ce abu ne mai matukar muhimmanci taimaka wa marasa lafiya su samu "mu'amaloli masu ma'ana da jama'a".
Babu wani cikin mutanen da aka bibiyi rayuwarsu da ke da cutar matsananciyar mantuwa a farkon gwaji, sai dai a tsawon lokacin da ake ci gaba da gwaje-gwajen an gano mutum 220 na da ita.
Rukunin masu binciken ya kwatanta halayyar mutanen da suke da cutar matsananciyar mantuwa da wadanda ba su da ita da nufin gano alamomi kan yadda huldarsu da jama'a ke da nasaba da hatsarin kamuwa da ita.
Wani bincike ya ce idan ana batu kan abin da ya danganci abota, to dankon zumunci ya fi tasiri a kan yawan abokai.
Farfesa Eef Hogervorst ta ce: "Mutane na iya kasancewa a kusa da kai, amma adadin aminai na kukut ne ke da alaka da raguwar hatsarin kamuwa da cutar mantuwa... ba wai yawan abokai ba."
Ta ce tana jin samun abokai na kukut ka iya kasancewa "shamaki" daga matsalar nuƙurƙusar jiki, wadda ke da alaƙa da raunin lafiya.
Sabubba tara da ke janyo hatsarin cutar mantuwa
Kurumcewa a shekarun manyanta - na sanadin kashi 9% na hatsarin kamuwa
Gaza kammala karatun gaba da sakandare - 8%
Shan taba sigari - 5%
Gaza neman maganin sirewar rayuwa tun wuri - 4%
Rashin katabus - 3%
Ware kai daga jama'a - 2%
Hauhawar jini mai tsanani - 2%
Taiba - 1%
Ciwon suga rukuni na 2 - 1%
Wadannan sabubba - da aka bayyana, na cikin jerin wadanda ake iya sauyawa - sukan hadu su kasance kashi 35 cikin 100.
Ana jin ba a iya sauya sauran sabubban da ke haddasa cutar mantuwa wadanda su ne da ke da kashi 65 cikin 100.
Nazarin kuma ya nuna cewa mutanen da ke rayuwar gwaurontaka na da ninki biyu na hatsarin kamuwa da cutar mantuwa a lokacin binciken idan an kwatanta su da masu aure.
Ana da masaniyar cewa cutar mantuwa na fara shafar kwakwalwa ne shekaru gommai kafin a gano ta, ta hanyar gwaje-gwaje kuma wasu daga cikin sauye-sauyen farko da mai cutar ke samu na hana mutum mu'amala da jama'a.
Ko ma dai yaya abin yake, daraktan bincike a gidauniyar tallafa wa masu cutar kuncewar tunani, Dr Dough Brown na cewa kadaici wani gagarumin abu ne wajen haddasa cutar mantuwa.
Source: BBC Hausa
Title :
Aure Kan Iya Hana Samun Cutar Mantuwa-Bincike
Description : Aure da yin abokai ko kawaye na kukut ka iya taimakawa wajen hana kamuwa da cutar mantuwa a cewar masu bincike na Jami'ar Loughborough a...
Rating :
5