Hukumar zabe ta jihar Adamawa ta sanar cewa tayi wa ‘yan gudun hijira da suka dawo gida 1,947 rajistan sabbin katin zabe.
Kwamishinan hukumar na jihar Adamawa Kassim Gaidam ya sanar da hakan a garin Yola ranar Laraba.
Ya ce hakan ya yiwu ne ganin cewa zaman lafiya ya dawo jihar.
Ya ce da bisani dole suka dakatar da yi wa mutane rajistan katin zabe saboda aiyukkan Boko Haram.
‘‘Mun fara gudanar da rajistan katin zaben ne a watan da ya gabata bayan tabbacin tsaron da muka samu daga wajen jami’an tsaro’’.
Gaidam ya ce a yanzu hakan sun yi wa mutane 103,000 rajistan katin zabe a jihar sannan suna wayar da kan matasa musamman ‘yan makarantan sakandare kan yadda za su yi zabe cikin kwanciyar hankali.
Source: Premium Hausa
Title :
Anyiwa 'Yan Gudun Hijiran Dasuka Dawo Katin Zabe A Adamawa
Description : Hukumar zabe ta jihar Adamawa ta sanar cewa tayi wa ‘yan gudun hijira da suka dawo gida 1,947 rajistan sabbin katin zabe. Kwamishinan hukum...
Rating :
5