Gagarumin hadari ya jawo ruwan sama mai yawa da kuma walkiya mai ban mamaki ba kakkautawa a birnin Queensland da ke kasar Australiya.
A lokacin da hadarin ya hadu an shafe sa'o'i da dama ana ta walkiya mai karfi ba kakkautawa a sararin samaniya, inda aka shafe tsawon dare ana yin walkiyar har sai da aka yi ta sau sama da 176,000.
Kuma ana sa ran za a sake wasu jerin walkiyar a ranar Litanin.
Ofishin hukumar kula da yanayi a birnin Queensland, ya yi gargadin cewa da akwai hadari mai dauke da tsawa mai tsanani da iska mai karfi da zai yi barna har da ruwa da kankara.
Ruwa mai tafe da iska da walkiyar ya barnata gidaje tare da barin daruruwan muhallai babu wutar lantarki.
Da akwai hotunan iskar hadarin mai karfi ta yadda ta mamaye samaniya, wadanda aka dauka da suka nuna yadda walkiyar ta wakana.
''Sararin samaniya ya murtuke na tsawo sa'o'i ba kamar yadda aka saba gani ba a lokacin haduwar hadari," in ji mai daukar hoto a Brisbane, Steph Doyle, kamar yadda ya shaida wa BBC.
"Hadarin na taruwa ya narke abun da ke jawo walkiya ba kakkautawa baki daya a sararin samaniya," a cewarsa.
Source: BBC Hausa
Title :
Anyi Walkiya Sau 176,000 A Dare Daya A Australia
Description : Gagarumin hadari ya jawo ruwan sama mai yawa da kuma walkiya mai ban mamaki ba kakkautawa a birnin Queensland da ke kasar Australiya. A lok...
Rating :
5