A daidai lokacin da ake zabe a wasu sassan Kenya, wasu sassa kuma irin su Kisumu zanga-zanga ake yi, kuma ko kuri'a daya ba a kada ba.
Yawancin titunan da ke cikin birin a toshe suke da duwatsu da tayoyi da suke ci da wuta yayin da masu zanga-zanga ke arangama da jami'an tsaro - suna musayar duwatsu da hayaki mai sa hawaye.
Kawo yanzu dai ba a kada kuri'a ko daya ba a birnin, kuma cikin jami'an hukumar zabe 400 da ake tsammani za su zo, guda uku ne kawai suka zo.
Kazalika babu ko akwatin zaben da aka ajiye a runfunan zabe.
Lamarin haka yake a unguwannin marasa galihu da ke Nairobi inda 'yan adawa ke da rinjaye.
Amman a wasu sassan kasar ana ci gaba da gudanar da zabe, duk da cewa da alama mutane ba su fito kamar yadda suka fito ba a zaben watan Agusta wanda kotun kolin kasar ta soke.
Ana kyautata zaton cewa za a nemi alkalai su yanke hukunci kan ko za a iya amincwa da sakamakon zaben ko kuma a'a.
'Yan sanda sun yi arangama da magoya bayan 'yan adawa inda wasu daga cikinsu suke kokarin hana mutane zuwa rumfunan zabe.
An ayyana Shugaba Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi a watan Agusta, amman ana sake zaben ne domin zargin "magudi".
Wakilin BBC, Alastair Leithead da ke Nairobi ya ce da alama fitowar mutane domin kada kuri'a bai kai na zaben da aka yi a karon farko ba.
Mista Kenyatta yana neman wa'adi na biyu. Jagoran 'yan Adawa Raila Odinga ya janye daga takarar.
An fara zaben ne ranar Alhamis da misalin karfe 06:00 (karfe 03:00 ke nan na tsakar dare a agogon GMT) inda aka tura dubban 'yan sanda da sauran jami'an tsaro domin su kare masu zabe da rumfunan zabe.
Masu sa ido na kasa da kasa sun rage yawonsu saboda dalilan tsaro.
Wakilin BBC Emmanuel Igunza ya ba da rahoton cewa 'yan sanda sun yi harbi a Kisumu da ke yammacin Kenya.
Mutum biyu sun ji ciwo - an harbi dukkansu a cinya.
Daya daga cikin wadanda suka ji ciwon dan shekara 15 ne dayan kuma dan shekara 21.
A yanzu haka ana ba su kulawa a asibiti.
Wakilinmu ya kara da cewa an harba hayaki mai sa hawaye domin a tsarwatsa mutane daga babban dandalin 'yan adawa.
Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce 'yan sanda sun yi ta harbin iska domin tarwatsa magoya bayan 'yan adawa a birnin Kisumu da ke yammacin kasar, da kuma unguwar Kibera da ke birnin Nairobi.
An kuma yi amfani da hayaki mai sa hawaye.
Wani jami'in zabe a Kisumu- garin jagoran 'yan adawa Raila Odinga - ya shaida wa BBC cewa biyu daga cikin jami'an rumfar zaben ne suka fito.
Wani mai zabe a unguwar marasa galihu ta Mathare da ke Nairobi, kuma dan tasi David Njeru, mai shekara 26, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa : "Nauyin kada kuri'a ya rataya a wuyana ne.
A wancan lokacin layin masu zaben ya yi tsawon gaske kuma na yi jiran sa'a shida domin yi zabe, amman yanzu mutane ba su da yawa.
'Yan sanda sun harba wa masu zanga-zanga hayaki mai sa hawaye a birnin Kisumu
An kashe kimanin mutum 70 a tashe-tashen hankula tun lokacin da aka ayyana Mista Kenyatta a matsayin wanda ya lashen zaben watan Agusta.
Mista Odinga ya so a jinkirta zaben, amman yunkurin ya ci tura bayan da alkalai biyu ne kawai suka halarci zaman kotun kolin kasar ranar Laraba cikin alkalai bakwai.
Source: BBC Hausa
Title :
Anyi Dauki Ba Dadi Tsakanin Jam'iyu Biyu A Kenya
Description : A daidai lokacin da ake zabe a wasu sassan Kenya, wasu sassa kuma irin su Kisumu zanga-zanga ake yi, kuma ko kuri'a daya ba a kada ba. ...
Rating :
5