Rundunar sojin saman Najeriya ta tura jiragen yakin sama da jami'anta zuwa Jos, babban birnin jihar Filato domin tallafa wa rundunar tabbatar da zaman lafiya da ke aiki a jihar.
Sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce hafsan sojin saman kasar, Air Marshal Siddique Abubakar ne ya bayar da umarnin tura jiragen yakin a wani mataki na bin umarnin Shugaba Muhammadu Buhari na cewa a dakile tashe-tashen hankula da ake samu a wasu sassan jihar.
Rundunar sojin saman ta tura jirgin sama samfurin L-39ZA da kuma jirgi mai saukar angulu samfurin EC-135, wadanda za su bayar da kariya ga rundunar da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Wannan dai ba shi ne lokaci na farko da rundunar sojin saman Najeriya za ta tura jiragen yaki wani bangare na kasar domin tallafa wajen tabbatar da zaman lafiya ba.
Wannan na zuwa ne sakamakon tashe-tashen hankulan da ake samu na baya-bayan nan, inda aka kashe a kalla mutum 35 aka kuma jikkata wasu da dama a hare-haren da aka kai wasu kauyuka a karamar hukumar Bassa a jihar Filato a ranar Lahadin da ta gabata.
Tun a lokacin ne kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi sojojin kasar a kan su tashi tsaye wajan daukar matakan dakile tashen-tashen hankula da suka dawo a jihar ta Filato.
Source: BBC Hausa
Title :
Antura Jiragen Yaki Jihar Filato
Description : Rundunar sojin saman Najeriya ta tura jiragen yakin sama da jami'anta zuwa Jos, babban birnin jihar Filato domin tallafa wa rundunar tab...
Rating :
5