Bama-bamai biyu sun fashe a babban birnin Somaliya, Mogadishu, mako biyu bayan mummunan harin bam din da ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutum 350.
Harin farko ya faru ne bayan da aka shigar da wata mota cikin wani otel.
Daga nan ne sai wadansu mahara suka yi wa ginin dirar mikiya.
Hari na biyu kuma ya faru ne kusa da tsohon ginin majalisar dokokin kasar.
Akalla mutum 17 aka kashe a wajen otel din lokacin da wasu bama-bamai guda biyu suka fashe gabanin 'yan ta-da-kayar-bayan su auka ginin ciki har da wata mata da yara.
Kungiyar al-Shabaab wadda aka zarga da kai harin makon jiya - ta ce ita ta kai harin.
Har yanzu 'yan ta-da-kayar-bayan na ci gaba da mamayar otel din.
Kungiyar ta al-Shabaab, ta ce ko kadan ba ita ta kai harin da aka kai a makonni biyu da suka shude ba a kasar, amma kuma ta ce ta zabi kai hari otel din ne saboda 'yan siyasa da jami'an tsaro na yawan zuwa wajen.
Tunda farko, an tsara gudanar da wani taro ne kan sha'anin tsaro a ginin a yau Lahadi kuma akwai jami'an leken asiri da na 'yan sanda da ma 'yan siyasa a ciki.
Source: BBC Hausa
Title :
Ansake Kai Harin Bam Mogadishu
Description : Bama-bamai biyu sun fashe a babban birnin Somaliya, Mogadishu, mako biyu bayan mummunan harin bam din da ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mu...
Rating :
5