An yi garkuwa da wasu mutum hudu da ake zargin 'yan kasar Biritaniya ne a jihar Delta ne da ke yankin kudancin Najeriya.
Kakakin ofishin 'yan sandan jihar Andrew Aniamaka, ya ce mutanen 'yan mishan ne da ke zama a wani kauye a yankin, inda suke ayyukan bayar da kiwon lafiya kyauta.
Cikin wadanda aka sace din har da wasu ma'aurata, inda da misalin karfe 2:00 na daren ranar Juma'a ne wasu 'yan bindiga suka dirar musu.
Mista Aniamaka ya ce ya zuwa yanzu dai kungiyar da ke kiran kanta Karowei wadda ake zargin ta da sace mutanen, ba ta bukaci kudin fansa ba tukunna.
Basaraken kauyen ya shaida wa BBC cewa 'yan mishan din likitoci ne da suka kwashe shekara goma suna zama a kauyen.
Garkuwa da mutane domin neman kudin fansa dai ya zamo ruwan dare a yankin na Naija-Delta mai albarkatun man fetur, kuma 'yan sanda na zargin akwai yiwuwar lamarin wani martani ne dangane da yakin da ake yi da ta'addanci a yankin.
Source: BBC Hausa
Title :
Ansace Turawa 'Yan Mishan A Nigeria
Description : An yi garkuwa da wasu mutum hudu da ake zargin 'yan kasar Biritaniya ne a jihar Delta ne da ke yankin kudancin Najeriya. Kakakin ofishi...
Rating :
5