An samu barkewar annobar kyandar biri a jihar Bayelsa da ke Kudu maso kudancin Najeriya, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Kwamishinan lafiya na jihar Ebitimitula Etebu, ya tabbatar wa da BBC cewa tuni aka kebe mutum 10 da suka kamu da cutar, ana kuma neman wasu da ake tunanin sun kamu don su ma a kebe su.
Sai dai kwamishinan bai tabbatar da wasu rahotannin da ke cewa mutum 10 sun mutu sakamakon kamuwa da cutar ba.
Mista Etebu ya ce tuni aka aike da samfurin kwayoyin cutar dakin gwaje-gwaje na Hukumar Lafiya Ta Duniya da ke Senegal don tantancewa, kuma sakamakon gwajin ne zai tabbatar ko annoba ce.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa daga cikin mutum 10 da aka kebe akwai wai likita, kuma a kalla mutum 49 ake nema don a kebe su wadanda ake zaton sun kamu da cutar
Cutar ta samo asali ne daga jikin biri da saura dabbobin da ke shiga jeji kamar su bera da kurege da barewa.
Sai dai duk da cewa gomman shekaru da suka gabata an sha fama da cutar ko a arewacin kasar ma, a shekarun baya-bayan nan an samu raguwarta sosai ta yadda ba a jin ko duriyarta.
Source: BBC Hausa
Title :
Annobar Kyandar Biri Ta Barke A Jihar Bayelsa
Description : An samu barkewar annobar kyandar biri a jihar Bayelsa da ke Kudu maso kudancin Najeriya, kamar yadda rahotanni suka bayyana. Kwamishinan la...
Rating :
5