Wasu mahara daga kasar Mali sun yi wa dakarun Nijar da na Amurka kwanton-bauna a garin Tongo Tongo da ke arewacin jahar Tillabery, inda suka kashe sojin Amurka uku da na Nijar biyar, wasu kuma ba a gansu ba a harin da aka kai ranar Laraba.
Rahotanni sun ce 'yan bindigar daga Mali sun kai farmaki ne garin da ke kan iyakar Nijar da Mali a ranar Laraba da yamma, amma dakarun Nijar da na Amurka da ke yankin suka koro su.
A yayin wannan raraka ne da dakarun na Nijar da Amurkar suka yi musu ne sai 'yan tawayen suka yi musu kwanton-bauna, suka halaka wasu, sannan kuma ba a ga wasunsu ba.
Ya zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani game da lamarin da hukumomin Nijar suka fitar.
Sojojin Amurka suna bayar da horo da sauran taimako ga takwarorinsu na Nijar domin taimaka musu a yaki da mayaka masu ikirarin jihadi, wadanda suka hada da reshen kungiyar Al Qaeda na Arewacin Afirka.
A wani rahoto da Majalisar dinkin duniya ta fitar a baya bayan nan ta ce hare-haren da masu kaifin kishin Islama ke kai wa dakarun gwamnatin Mali da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ma dakarun Faransa na kara karuwa matuka gaya.
An kai irin wadannan hare-hare guda 75 a tsakanin watan Yuni zuwa Satumbar da ya gabata, lamarin da ya rubanya na watanni hudu kafin watan Yunin.
An bayyana shirin wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya a Mali da cewa shi ne mafi muni a duniya.
Tasirin Kisan Sojin Amurka;
Kisan sojin Amurka ba karamin abu ba ne ga kokarin kasar na shiga ayyukan tabbatar da tsaro musamman a Afirka.
A shekarar 1992 lokacin da jirgin yaki mai saukar ungulu na Amurka da ake kira Black Hawk ya fado a babban birnin Somalia, Mogadishu, magoya bayan Mohammed Aideed suka rika jan gawar wani sojan Amurka da ya mutu a jirgin a titin birnin, tsirara suna wulakanta ta cikin murna.
Daga nan ne Shugaba Clinton na Amurka a lokacin ya haukra da farautar Mohammed Farah Aideed din, ya kawo karshen aikin tabbatar da zaman lafiyar a Somalia, lamarin da ya ci ran sojin Amurka Staff Saja William David.
Shugaban ya bayar da umarnin ficewar dukkanin sojin Amurka daga Somalia zuwa ranar 31 ga watan Maris na 1994, su ma sauran kasashen Yammacin duniya suka bi sahu.
A lokacin da sojin tabbbatar da zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya na karshe suka fice daga Somalia a 1995, bayan kashe sama da dala biliyan biyu, babu wata tabbatacciyar gwamnati a kasar.
Source: BBC Hausa
Title :
Ankashe Sojan Amurka Uku A Nijar
Description : Wasu mahara daga kasar Mali sun yi wa dakarun Nijar da na Amurka kwanton-bauna a garin Tongo Tongo da ke arewacin jahar Tillabery, inda suka...
Rating :
5