Akalla mutum 60 ne aka kashe a wasu hare-haren kunar bakin wake da aka kai kan wasu masallatai biyu a kasar Afghanistan, kamar yadda jami'an kasar suka bayyana.
Maharin farko ya kutsa wani masallacin 'yan Shia ne a birnin Kabul, babban birnin kasar, inda ya bude wuta kafin daga bisani ya ta da bama-baman da ke jikinsa.
Harin ya kashe kusan mutum 40 ciki har da mata da kananan yara.
Akalla mutum 20 ne kuma suka mutu yayin da wani maharin ya ta da bam a wani masallacin a gundumar Ghor.
Kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai hare-haren.
Source: BBC Hausa
Title :
Ankashe 'Yan Shia 60 A Masallaci A Afghanistan
Description : Akalla mutum 60 ne aka kashe a wasu hare-haren kunar bakin wake da aka kai kan wasu masallatai biyu a kasar Afghanistan, kamar yadda jami...
Rating :
5