An kashe akalla mutum biyar a kudancin Malawi bayan an zarge su da nuna wasu dabi'u irin na fatalwa.
Shugaban kasar Malawi Peter Mutharika ya lashi takobin kaddamar da wani bincike kan wadannan kashe-kashe.
Gwamnati ta sanya dokar hana fitar dare don hana kungiyoyin 'yan sintiri masu a ture kashe karin mutane.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta janye ma'aikatant daga cikin wasu larduna guda biyu a daidai lokacin da tsoron fatalwa ya mamaye kudancin kasar.
Ana zargin mutanen da aka kashe da shan jinin dan'adam a wani bangare na ayyukan matsafa.
Dokar takaita fitar dare da gwamnati ta sanya na aiki ne tsawon sa'a goma.
A lokaci guda kuma, ofishin shugaban kasa ya fada a cikin wata sanarwa cewa: "Wannan al'amari ya janyo gagarumar damuwa ga shugaban kasa da kuma illahirin gwamnati."
Majalisar Dinkin Duniya a cikin wani rahoto ta ce ga alama jita-jitar ganin fatalwa ta faro ne daga kasar Mozambique, inda ta "bazu zuwa" lardunan kan iyakar Malawi na Mulanje da Phalombe.
Sai dai ya ce babu tabbas a kan ko mene ne ya rura wutar jita-jitar.
"An dakatar da aikace-aikacen Majalisar Dinkin Duniya na wucin gadi ne ya zuwa lokacin da al'amura za su inganta," a cewar rahoton.
A matsayinta na daya daga cikin kasashe mafi talauci, hukumomin ba da agaji da kungiyoyi na aiki a Malawi.
Kasar na fama da faduwar matsayin ilmi, inda imani da maita ke yaduwa kuma kasar a kai-a kai na samun kanta cikin jita-jitar ganin "fatalwa".
A shekara ta 2002 ma an samu barkewar tarzomar 'yan sintiri mai alaka da jita-jitar ganin fatalwa.
Source: BBC Hausa
Title :
Ankashe Mutum Biyar Saboda Nuna Halayen Fatalwa
Description : An kashe akalla mutum biyar a kudancin Malawi bayan an zarge su da nuna wasu dabi'u irin na fatalwa. Shugaban kasar Malawi Peter Muthar...
Rating :
5