Akalla mutum 35 aka kashe yayin da aka jikkata wasu da dama a hare-haren da aka kai wasu kauyuka a karamar hukumar Bassa a jihar Filato.
Wasu 'yan bingida ne dai suka kai hare-haren a ranakun Lahadi da kuma Litinin, inda suka lalata gidaje da dama.
Rahotanni sun ce hukumomi sun sanya dokar takaita zirga-zirga a yankin inda aka tura karin jami'an tsaro.
A halin yanzu manyan jami'an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a jihar Filato suna tattauna yadda za a kawo karshen tashe tashen hankula.
Mutane da dama ne suka mutu a 'yan shekaru baya a tashe tashen hankula masu nasaba da kabilanci da addini a jihar.
Sai dai a 'yan watannin baya, an samu kwanciyar hankali a jihar bayan yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma da bangarorin da ke rikici da juna.
Source:BBC Hausa
Title :
Ankashe Mutum 30 A Jihar Filato
Description : Akalla mutum 35 aka kashe yayin da aka jikkata wasu da dama a hare-haren da aka kai wasu kauyuka a karamar hukumar Bassa a jihar Filato. Wa...
Rating :
5