An kashe wasu masu gadi biyu aka kuma raunata wasu uku a wani hari da wani dan bindiga ya kai kan wata fadar Masarautar Saudiyya a Jeddah.
Ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta Saudiyyar ta ce, maharin wanda yana dauke ne da bindiga mai sarrafa kanta da kuma bama-bamai na fetur, wato hadin gida, shi ma an harbe shi.
Bayan binciken da aka yi an gano cewa mutumin mai shekara 28, dan kasar ne kuma sunanshi Mansour al-Amri.
Lamarin ya faru ne, da misalin karfe uku da minti 15 agogon kasar (daya da minti 15 agogon Najeriya). a wani wurin binciken ababan hawa a wajen kofar shiga fadar ta Al Salam, inda ya tuka motarsa har zuwa wurin sannan ya bude wuta.
A halin da ake ciki dai Sarki Salman na Saudiyyar yana kan wata ziyara ta kasashen waje. Kawo yanzu babu wani karin bayani da aka bayar na game da dalinlin maharin na kai wannan farmaki.
Kafin wannan harin ofishin jakadancin Amurka ya yi gargadi ga 'yan Amurkar da ke kasar a ranar Asabar, da su yi takatsantsan wurin zuwa unguwar, bayan wasu rahotanni da ba a tabbatar ba na kai hari a yankin.
A 'yan kwanakin da suka gabata 'yan sandan Saudiyyar sun yi wa wasu wurare uku dirar mikiya, a babban birnin kasar Riyadh, wadanda ke da alaka da wata kungiya da ake zargi ta 'yan ta'adda ce, mai dangantaka da kungiyar IS, wanda a lokacin suka kashe mutane biyu, sannan suka kama wasu biyar.
Source: BBC Hausa
Title :
Ankashe Masu Gadin Masarautar Saudiyya A Wani Harin Bindiga
Description : An kashe wasu masu gadi biyu aka kuma raunata wasu uku a wani hari da wani dan bindiga ya kai kan wata fadar Masarautar Saudiyya a Jeddah. ...
Rating :
5