Hukumomi a Afrika ta Kudu sun tsare wani mai gadi bisa zarginsa da laifin cin zarafin yara 'yan firamare mata su 54.
A ranar Litinin aka soma bincike kan batun, bayan da wasu dalibai mata biyu suka kai kara, kuma tuni gwamnati ta tura jami'ai zuwa makarantar da ke Soweto a kudancin Johannesburg.
Yara 'yan mata biyu 'yan shekaru 8 da kuma 12 ne suka je ofishin 'yan sanda a ranar Litinin ---- inda suka kai kara cewa wani mai gadi ya yi lalata da su a wata makarantar firamare da ke Soweto.
Tun lokacin da aka soma bincike, ----sai aka gano cewar mutumin ma ya ci zarafin dalibai mata 52.
Kuma ya shafe watai 18 yana tafka ta'asar.
A ranar Laraba ne ake sa ran mai gadin zai bayyana gaban wata kotun Majistre a Soweto.
A halin yanzu kuma sashen ilimi na yankin ya tura jami'ai domin taimakawa 'yan yaran da aka ci zarafinsu sannan kuma a fadada bincike.
Afrika ta Kudu ta kasance daya daga cikin kasashe da aka fi aikata fyade da kuma cin zarafin mata a duniya.
Source: BBC Hausa
Title :
Ankama Mai Gadin Dayayi Lalata Da Yara Mata 54
Description : Hukumomi a Afrika ta Kudu sun tsare wani mai gadi bisa zarginsa da laifin cin zarafin yara 'yan firamare mata su 54. A ranar Litinin ak...
Rating :
5