Hukumomin lafiya a Najeriya sun gargadi al'ummar kasar da su kiyayi cin naman biri da sauran naman dabbobin daji, bayan da aka samu barkewar annobar cutar kyandar biri a jihar Bayelsa da ke kudancin kasar.
A kalla mutum 10 ne ma'aikatar lafiya ta kasar ta tabbatar da cewa sun kamu da cutar, kuma tuni a ka kebe su don gudun kada ta yadu.
A wata sanarwa da ya fitar, ministan lafiya na kasar Isaac Adewole, ya ce ana bincike kan abin da ya jawo cutar, wadda ake samun ta daga jikin birrai da bera da kurege da kuma barewa.
Sai dai ministan ya ce, duk da cewa ba a san takamaimai maganin cutar ba, al'amarin ba na daga hankali ba ne sosai saboda cutar ba mai tsanani ba ce.
Sai dai ya yi kira ga jama'a da su kiyaye bin hanyoyin kamuwa da cutar, "kamar cin naman biri da sauran naman daji su kuma kiyaye shiga waje mai taron jama'a sosai."
Mista Adewole ya ce kwayar cutar na daga cikin dangogin cututtuka kamar karanbau da bakon-dauro.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, daga cikin mutum 10 da aka kebe akwai wani likita, kuma a kalla mutum 49 ake nema don a kebe su wadanda ake zaton sun kamu da cutar.
Ba a faye samun annobar cutar kyandar biri ba amma kuma ba ta faye hallaka mutane ba.
Source: BBC Hausa
Title :
Anhana 'Yan Nigeria Cin Naman Biri
Description : Hukumomin lafiya a Najeriya sun gargadi al'ummar kasar da su kiyayi cin naman biri da sauran naman dabbobin daji, bayan da aka samu bark...
Rating :
5