An yanke wa wata mahaifiya hukuncin zaman gidan kaso na tsawon kwana bakwai a jihar Michigan ta kasar Amurka, saboda ta saba umarnin kotu na kai danta allurar rigakafi.
Rebecca Bredow, ta ki yarda a yi wa dan nata rigakafin ne bayan kuma sun yi yarjejeniya da mahaifinsa a kan za ta kai shi a yi masa.
Yanzu haka dai an ba wa mahaifin yaron damar ci gaba da rike shi na wucin-gadi har sai an yi masa allurar.
Doka ta ba wa iyayen yara a jihar Michigan damar tsallakewa ko kuma jinkirta yi wa yara allurar rigakafi saboda wata akida da suka yarda da ita.
To amma ita Mrs Bredow, ta saba wa doka ne saboda ta karya alkawarin da suka yi da tsohon mijinta tun a watan Nuwambar shekarar 2016, na tabbatar da an yi wa yaron allurar rigakafin.
Wani bincike da Mlive ta gudanar, ya gano cewa jihar Michigan na daya daga cikin jihohin da ke samun koma baya wajen yi wa yara allurar rigafi a kasar Amurka, inda aka sanya ta a matsayin jiha ta 43 a cikin jihohin kasar 50.
Source: BBC Hausa
Title :
Andaure Uwa Saboda Kin Kai Danta Rigakafi
Description : An yanke wa wata mahaifiya hukuncin zaman gidan kaso na tsawon kwana bakwai a jihar Michigan ta kasar Amurka, saboda ta saba umarnin kotu na...
Rating :
5