An daure wani dan kasar Italiya mai cutar kanjamau tsawon shekara 24 a gidan yari bayan samunsa da laifin yad'a cutar da gangan ga mata har talatin ta hanyar jima'i ba tare da kariya ba.
An zargi mutumin wanda akanta ne dan shekara 33, Valentino Talluto da yada cutar ga 'yan matan da yake gamuwa da su ta shafukan samartaka na intanet tsawon shekara goma bayan ya kwan da sanin yana da kwayoyin cutar.
Masu bincike sun ce akwai maza guda uku samarin irin wadannan mata da su ma suka harbu, baya ga wani jariri na hudu.
Lauyoyi masu kare mutumin sun ce ayyukan Talluto rashin kiyayewa ne amma ba ganganci ba.
Mahaifiyar Valentino wadda 'yar shaye-shaye ce, ita kanta ta kamu da cutar ta HIV , inda kuma ta mutu a lokacin yana da shekara hudu da haihuwa.
Source: BBC Hausa
Title :
Andaure Mutumin Dayasa Wa Mata 30 Cutar Kanjamau
Description : An daure wani dan kasar Italiya mai cutar kanjamau tsawon shekara 24 a gidan yari bayan samunsa da laifin yad'a cutar da gangan ga mata ...
Rating :
5