A Najeriya, hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mace 1 yayin da aka ceto mutum 19 a hatsarin jirgin ruwa a Legas.
Hatsarin ya auku ne da safiyar Talata lokacin da jirgin ruwan dauke da fasinjoji 21 ya taso daga Ikorodu zuwa Ebutte Ero ya kuma ratsa gadar Third Mainland da ke birnin Legas.
Rahotanni sun ce 'yan sanda sun tsare direban jirgin ruwan tare da mai taimaka masa bayan sun tsere sun bar fasinjoji lokacin da hatsarin ya auku.
A 'yan watannin nan an sha samun aukuwar hatsarin jiragen ruwa a wasu sassan Najeriya, lamarin da kan kai ga asarar rayuka da dukiyoyi.
Sai dai masu lura da al'amura na danganta aukuwar hatsarin jiragen ruwa da cunkoson da ake yi musu, ta hanyar daukar mutane da kaya fiye da kima da kuma rashin yashe kogunan da ake sufuri a cikinsu.
Source: BBC Hausa
Title :
Anceto Mutum 19 A Hatsarin Jirgin Ruwa A Legas
Description : A Najeriya, hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mace 1 yayin da aka ceto mutum 19 a hatsarin jirgin ruwa a Legas...
Rating :
5